Mataimakin shugaban Ghana, Mahamudu Bawumia, ya gargadi ‘yan kasar a kan matsanancin halin tsadar rayuwa da za a shiga yayin da kasar ke neman bashin Asusun bayar da tallafi na duniya bayan da hauhawar farashi ta kai kashi 29.8 cikin dari a watan Yuni.
A ranar Laraba ne jami’an Asusun na IMF suka kammala ziyararsu domin nazarin irin yanayi da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki tare kuma da tattaunawa kan tallafin.
Gwamnatin kasar ta dora alhakin halin da ake ciki a kan matsaloli na waje, wadanda suka hada da yakin Ukraine. In ji BBC.
Mista Bawumia ya gaya wa ‘yan jarida cewa : “Yayin da muke fatan a gaggauta kawo karshen yakin [Ukraine], dole ne mu san cewa abubuwa za su iya yin tsanani kafin a samu sauki. Wajibi ne mu shirya domin fuskantar hakan.”
Ya kara da cewa, ”Babban matakin gaggawa da ya kamata a dauka shi ne dawo da tsimi da tsantseni a kan kudi da basuka, wannan kuma zai kasance ne ta hanyar haraji da kudaden da gwamnati ke kashewa da kuma yin sauye-sauye.”