fidelitybank

Ku kori jami’an da baku da ƙwarin gwiwa a kan su – Rundunar Sojoji

Date:

Shelkwatar tsaro ta fitar da wani gargadi ga wasu jami’anta da ake zargi da nuna rashin da’a da nuna wasu munanan dabi’u.

Har ila yau, ta umurci shugabannin sojojin Najeriya, na ruwa da na sama, da su ‘kori’ jami’an da basu da kwarin guiwa a kansu, wajen sauke nauyin da ke kansu na hidimtawa kasa.

Umarnin na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Mayun da ya gabata, mai dauke da sa hannun daraktan harkokin gudanarwa na ma’aikatar tsaron Najiyar Rear Admiral Muhammed Nagenu, a madadin babban hafsan hafsoshin tsaron kasar Janar Lucky Irabor.

Shima kakakin ma’aikatar Major Akpon ya tabbatar da wannan wasika, sai dai ya ce ba wai za a kori sojojin ban aa aiki, illa dai gargadi irin na gyara kayanka, domin a cewarsa dabiu irin wadannan na iya haifar a rashin kwarin guiwa a kansu, musamman ta fuskar tura su fagen fama don tunkarar matsalolin tsaron da suka addabi kasar.

Ta ce a yayin da take ke iya bakin kokarinta wajn yaki da matsalolin taron da ake fuskanta, rashin maida hankalin wadannan dakaru na iya maida hannun agog baya, a don haka ko su gyara, ko kuma yi musu ritayar, tunda zai rage babu wani zabi da ya wuce hakan.

Birgedya Janar Sani Usman Kuka Sheka, mai sharhi ne kan lamuran tsaro a Najriya, ya kuma ce akwai abubuwan cikin gida da wasu bata gari suke fita suna yadawa ga mutanen waje, ana haka a aikin damara, amma ba a korar mutum haka kurum, sai an bi wasu hanyoyi masu yawa, kuma in da hakkokin mutum sai an biya shi hakkokinsa.

Wannan dai na faruwa ne yayin da ake unkarar zabukan 2023, kuma a cewar Birgediya Janar Sani Usman Kuka Sheka, dama akan yi gargadi irin wannan a lokaci irin wannan da aka shiga harkokin siyas.

nigeria.news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp