Al’ummar garin ‘Yar Katsina a jihar Zamfara mai fama da rikicin ‘yan fashin daji, sun yi kira ga hukumomi su kai musu ɗauki don kuɓutar da gomman mata da ƙananan yaransu da aka sace tsawon kwana 18.
Bayanai sun ce, ƴan fashin daji sun kai hari yankin na ƙaramar hukumar Bungudu ne tare da sace mata da yara fiye da 100 a ranar 5 ga wannan wata, kafin sako ƙalilan cikinsu daga bisani.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ce, ko da yake, ba ta da tabbaci kan adadin matan da aka sace daga garin na ‘Yar Katsina, amma tana yin duk mai yiwuwa wajen ganin ta kuɓutar da duk mutanen da ke hannun ‘yan fashin daji a faɗin jihar. In ji BBC.