Gwamnatin tarayya ta gargadi mambobin kungiyar likitoci ta kasa NARD da su janye yajin aikin gargadi na kwanaki biyar da suke yi.
Sen. Chris Ngige, Ministan Kwadago da Aiki ne ya yi wannan gargadin ranar Talata a Abuja, jim kadan bayan samun takardar sanarwa daga hukumar gudanarwar NARD kan yajin aikin da ta shirya yi.
Ngige ya bayyana hakan ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mista Olajide Oshundun, Daraktan yada labarai da hulda da jama’a a ma’aikatar, inda ya bayyana yajin aikin da aka shirya a matsayin wanda ya sabawa doka.
Karanta Wannan:Â Kungiyar Likitoci masu neman kwarewa sun tsunduma yajin aiki
Ana sa ran za a fara aikin masana’antu na gaba da tsakar daren ranar 16 ga Mayu.
Ngige, wanda ke mayar da martani ga wasikar da aka kai ofishinsa da misalin karfe 5 na yammacin ranar, ya ce ya tuntubi Ministan Lafiya, wanda ya shaida masa cewa an shirya ganawa da likitocin da ke wurin a ranar Laraba.
Don haka ya shawarci likitocin da su yi amfani da damar da suka samu wajen tattaunawa da ma’aikatansu, maimakon shiga yajin aikin gargadi, wanda doka ba ta sani ba.
A cewar sa, “Zan ba su shawarar su halarci taron da Ministan Lafiya a gobe. Zan kuma ba su shawara mai karfi da kar su shiga yajin gargadi na kwanaki biyar.
“Idan ba ku yi aiki ba, ba za a biya ku ba,” in ji shi.
Dangane da batun biyan MRTF na gaggawa ga mambobinsu, ya ce an kasafta a cikin kasafin kudin 2023, amma har yanzu ba a fitar da shi ba, saboda har yanzu kasafin 2022 na ci gaba da aiki, ya ce wadanda ke 2022 duk an biya su.
Ngige ya musanta ikirarin da NARD ta yi na cewa Gwamnatin Tarayya ba ta biya mafi karancin albashin ma’aikata ba.
Ya kara da cewa duk ma’aikatan da ke bangaren ilimi da lafiya, har ma da hukumomin tsaro sun ci gajiyar wannan gyara.