Hukumar da ke kula da hada-hadar hannayen jari ta kasa SEC, ta gargadi masu son zuba jari da su guji zuba jarin su na fitaccen mawakin nan, David Adeleke wanda aka fi sani da Davido.
Hukumar ta ce saka hannun jari a cikin tsabar kudin $Davido yana da haɗari, saboda tsabar kuɗin na memecoin ne da ba su da ƙima mai mahimmanci kuma hasashe ne kawai.
Sanarwar da hukumar ta fitar a ranar Juma’a ta ce, ba ta gane tsabar kudin ba.
Sanarwar ta kara da cewa, an jawo hankalin Hukumar Kula da Harkokin Kasuwanci ta kasa na memecoin da aka sani da “$ Davido” da ake zargi da alaka da shahararren mawakin.
Har ila yau, tsabar kudin na Memecoin ba a yi niyya ya zama hanyar musayar kuɗi da jama’a suka karɓa a matsayin biyan kudi ba.