Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya gargadi al’umma da su guji boye masu laifi da wadanda ake zargi da aikata laifuka a tsakanin su yayin da gwamnati ke kokarin magance matsalar rashin tsaro a jihar.
El-Rufai ya yi wannan gargadin ne a jiya a lokacin da ya ziyarci basaraken Kagoro, Ufuwai Bonet a fadarsa da ke karamar hukumar Kaura, domin jajanta masa kan harin da aka kai a yankin.
El-Rufai ya kalubalanci sarakunan gargajiya da su kara kaimi wajen sauke nauyin da ke kansu na samar da shugabanci