fidelitybank

Ku dauki makamai ku kare kan ku daga ‘yan bindiga – Gwamnan Bauchi

Date:

Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, ya umarci al’umomin yankunan da aka kai wa hari a baya-bayan nan a yankin ƙaramar hukumar Alkaleri da su tashi tsaye, su nemi makamai domin su kare kansu daga farmakin ‘yan bindiga.

Jaridar Daily Trust, ta ambato gwamnan na faɗin haka a fadar hakimin Yelwan Duguri a lokacin da ya ziyarci ƙauyukan Rimi da Gwana da Yalwan Duguri domin jajanta musu game da hare-haren ‘yan bindiga.

Dagacin garin Yelwan Duguri, Alhaji Adamu Mohammed Duguri ya ce mutum 20 ne suka mutu a ƙauyen Rimi lokacin da ‘yan bindigar suka kai hari garin.

Gwaman ya ce lamarin abu ne da ‘ba za a lamunta ba’ dan haka dole ayi duk abin da ya kamata, domin hana faruwar hakan a nan gaba.

”An san ku da jarunta, bai kamata ku bar mutanen nan su ci gaba da cutar da ku ba, dan haka ku kare garinku domin ƙwatar kawunanku, ya kamata ku tashi tseye, ku nemi makamai domin kare kanku”, in ji gwamnan.

Haka kuma ya shawarci mutanen da su zaƙulo ɓata-gari a cikin mutanen da ke haɗa kai da ‘yan bindiga, musamman waɗanda suke bai wa ‘yan bindigar bayanan sirri kan mutanen gari, yana mai cewa dole sai da ɗan gari akan ci gari.

Wannan dai ba shi ne karo na farko da wani gwamna a Najeriya ke umartar al’umma da su nemi makamai domin kare kansu ba.

Domin kuwa a shekarar 2021 ma gwamnan jihar Katsina da ke arewa maso yammacin ƙasar Aminu Bello Masari ya umarci al’ummar jiharsa da su nemi makamai domin kare kansu daga hare-haren ‘yan bindiga.

nigerian 
news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Hisbah za ta yi wa ‘yan Daban Kano aure

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta sanar da wani...

Ganduje ya dawo Najeriya bayan ya shafe wata guda a Landan

Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Ganduje,...

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...
X whatsapp