Sabbin sulalla masu kan Sarki Charles na III sun bayyana, da kwabo 50 dauke da hoton sabon sarkin zai shiga hannun jama’a nan da ‘yan makonni.
BBC ta samu izinin farkon ganin kwabo 50 da tsabar fam biyar wanda ya hadar da hoton Sarki wanda wai masassakin Burtaniya Martin Jennings.
Sabbin kwabbunan sun zo ne da al’adar tsawon karni da yawa inda yanzu fuskar basaraken take kallon hagu – sabanin magabaciyarsa.
Sai dai ba kamar Sarakunan Burtaniya da suka gabata, da kuma Sarauniya ba, hoton ba ya dauke da kambun sarauta.
Sarki Charles ne da kansa ya amince da surar da aka buga a kan kwabban, kuma an fahimci ya yi na’am da su.