Shugaban kasa Muhammdu Buhari, ya shawarci ‘yan ƙasa da su bi ra’ayinsu wajen zaɓar shugabanni na gari, a ɓangaren zartarwa da na majalisa, yana mai cewa zamanin sayen ƙuri’a ya wuce.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban ƙasar Malam Garba Shehu ya fitar, jim kaɗan bayan shugaban ƙsar ya kaɗa ƙuri’a, Muhammadu Buhari ya ce a yanzu mutane sun waye da zaɓen ra’ayinsu.
“Ina sane yanzu ba kamar da ba ne, mutane ba su da kuɗin da za su ja ra’ayin masu kaɗa ƙuria, kamar yadda suke yi a baya. A yanzu idan mutum ya kawo kuɗi, mutane za su karɓa kuma su zaɓi ra’ayinsu.
Karanta Wannan: Buhari ya kada kuri’arsa a Daura
Shugaba Buhari ya yaba wa kafofin yaɗa labaran ƙasar bisa rawar da ya ce sun taka wajen wayar da kan ‘yan ƙasar wajen sanin haƙƙokinsu a matsayinsu na ‘yan ƙasa, tare da samar musu kafar kalubalantar shugabanninsu kan alƙawuran da suka ɗaukar musu.
”Kafofin yaɗa labarai suna yin abin da ya dace wajen wayar da kan mutane, tare da ba su damar tofa albarkacin bakinsu. Za ka ji ana yi wa shugabanni tambayoyi masu tsauri a lokutan da ake hira da su a gidajen talabijin da radiyo da sauran kafofi, kuma a kodayaushe ‘yan jarida na tabbatar da cewa an amsa waɗannan tambayoyi”.
Daga ƙarshe shugaban ya ce bai yi mamakin nasarar da Bola Ahmed Tinubu ya samu a zaɓen shugaban ƙasar da ka gudanar ranar 25 ga watan Fabrairun da ya gabata ba.