Gwamnatin Zamfara, ta bai wa dukkan ‘yan Jihar damar mallakar bindiga, domin kare kansu daga ‘yan fashin daji da masu garkuwa da mutane.
A wata sanarwa da Kwamishinan yaɗa labaran Jihar, Ibrahim Magaji Dosara, ya aike wa manema labarai ranar Asabar, ya ce, gwamnati ta dauki matakin ne sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan ta’adda da ‘yan fashin daji.
Gwamnatin Zamfara ta dauki matakin ne watanni da dama bayan gwamnatin Jihar Katsina da ke makwabtaka ta umarci mazauna jhar su mallaki bindiga, domin kare kansu daga masu kai hare-hare.
“Hare-haren ta’addanci sun kasance abin damuwa ga jama’a da gwamnatin jiha. Don haka ne, domin mu magance wannan matsala baki daya a yankunan mu, gwamnati ba ta da zabin da ya wuce daukar matakan da suka hada da bai wa mutane damar shiryawa da kuma mallakar bindigogi domin kare kansu daga ‘yan fashin daji,” in ji sanarwar.