Hukumar tsaro ta NSCDC reshen jihar Jigawa, ta gargadi al’ummar jihar da su kasance masu lura da tsaro tare da kai rahoton duk wani motsi da suka samu a kusa da su musamman a lokacin bukukuwan ed-el Khabir.
Kwamandan NSCDC na jihar, Musa Alhaji Malah ne ya yi wannan kiran a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun mai magana da yawun hukumar CSC Adamu Shehu.
Ya ce rundunar ta tura jami’ai 1,125 domin samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin jama’a kafin bukin sallar Eid-el-Kabir, da kuma bayan bikin.
Kwamandan ya ce hakan ya yi daidai da umarnin kwamandan rundunar na samar da sa ido na tsawon sa’o’i 24 kan muhimman kadarorin kasa da ababen more rayuwa da kariya da kare rayukan fararen hula a fadin kasar nan.
A cewar sanarwar, “Kwamandan Musa Alhaji Malah (CC) ta hannun mataimakin kwamandan ayyuka DCC Kabiru Baffa ya ba da umarnin tura jami’ai da mazaje na musamman da sassa daban-daban na kananan hukumomi 27 na jihar nan take”.
Ya kuma umarci kwamandojin yankin, jami’an runduna, da kwamandojin sassan da su tabbatar da bin ka’idojin aiki.
Kwamandan, ya shawarci mazauna yankin da su kasance masu bin doka da oda tare da ba jami’an tsaro hadin kai don yin bikin ba tare da wata matsala ba.
Ya kuma kara musu kwarin guiwa da su kai rahoto ga jami’an tsaro mafi kusa.
Kwamandan a madadin daukacin hafsoshi da jami’an rundunar, ya yi wa al’ummar Jigawa fatan gudanar da bukukuwan Sallah lafiya a gaba.


