Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja a ranar Litinin, ta tanadi hukunci kan karar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya shigar na kalubalantar tsige shi da kotun sauraron kararrakin zabe ta yi.
Ku tuna cewa kwamitin alkalai uku karkashin jagorancin mai shari’a Oluyemi Akintan Osadebay ya kori Yusuf a ranar 20 ga Satumba, 2023.
Kotun ta bayyana kuri’u 165,663 na kuri’un Yusuf, saboda ba hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta sanya wa hannu ko tambari ba.
Sai dai a kotun daukaka kara a ranar Litinin, Wole Olanipekun, SAN, babban lauyan Yusuf, ya bukaci a yi watsi da hukuncin kotun.
Babban lauyan ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihi da wata kotu za ta soke zaben da aka yi kan rashin sanya hannu a bayan katin zabe.
Ya kara da cewa kotun ta yi kuskure, yana mai jaddada cewa wannan ne karo na farko da wata jam’iyyar siyasa za ta shigar da kara ba tare da shigar da dan takararta a matsayin jam’iyya ba kuma za a ayyana dan takarar a matsayin wanda ya lashe zaben.
Sai dai Lauyan jam’iyyar APC, Akin Olujimi, SAN, ya mayar da martani, inda ya ce kotunan daukaka kara ta bayyana karara cewa rashin sanya hannu kan kuri’u ya kasance na magudin zabe.
Kotun daukaka kara daga baya ta ajiye hukunci tare da sanar da cewa za a sanar da ranar ga bangarorin.