An baza jami’an tsaro a Kotun koli, yayin da ake sauraron kararraki uku na kalubalantar zaben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Jami’an tsaro dauke da muggan makamai sun killace kotun daga wasu lauyoyi da masu kara da ba su amince da su ba.
Sai dai lauyoyin Tinubu karkashin jagorancin Cif Wole Olanipekun SAN, na Atiku Abubakar, karkashin Chris Uche SAN, da na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), karkashin jagorancin Abubakar Mahmoud, aka ba su izinin shiga dakin Kotun.
A lokacin wannan rahoto, shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila; Mai baiwa kasa shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu; Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Abdullahi Umar Ganduje; Sakataren kasa, Sanata Bashir Ajibola; wasu biyar kuma sun zauna a cikin kotun.