Hukumomi a ƙasar Saudiyya sun wanke wasu ƴan Najeriya mata guda uku da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi.
Ma’aikatar harkokin wajen Najeriya ce ta fitar da sanarwar hakan, a jiya Lahadi, inda ta ce an kama su ne a ranar 5a ga watan Maris na shekarar 2024 a birnin Madina.
Sanarwar ta ce matan su ne: Hadiza Abba da Fatima Umater Malah da Fatima Kannai Gamboi, kuma an sake su ne bayan wata goma ana shari’a a ƙasar.
An kama matan ne bayan an kama wasu mutum biyu ƴan Najeriya da miyagun ƙwayoyi da suka haɗa da hodar ibilis, inda aka zargi matan da taimakonsu wajen shigar da ƙwayoyin zuwa ƙasar.
Sanarwar ta ƙara da cewa an miƙa matan ga ofishin jakadancin Najeriya da ke Saudiyya, kuma tuni aka fara shirye-shiryen mayar da su ƙasarsu Najeriya.