fidelitybank

Kotun MDD za ta yanke hukunci a kan hare-haren da Isra’ila ke kaiwa Gaza

Date:

A yau Juma’a ake saran kotun Majalisar Dinkin Duniya za ta yanke hukuncin da zai bukaci Isra’ila ta gaggauta kawo karshen ayyukanta na soji a cikin Gaza.

Shari’ar da ake gudanarwa a kotun hukunta manyan laifuka da ke Hague wani bangare ne na karar da Afirka ta Kudu ta shigar, da ke zargin Isra’ila da aikata kisan kare dangi kan Falasdinawa.

Isra’ila dai ta fito karara ta musanta wannan zargi kuma da alama za ta yi burus da duk wani hukuncin ko umarni daga wannan kotu.

Sai dai duk hukuncin da za a yanke kan bukatar tsagaita wuta zai kara matsin kaimi kan kiraye-kirayen da ake yi wa Isra’ila na ganin ta tsagaita wuta.

Fiye da Falasdinawa 25,000 – akasari mata da yara – aka kashe sannan dubbai sun jikkata, a cewar ma’aikatar lafiya ta Hamas da ke Gaza tun lokacin da Isra’ila ta soma mamayar da ta samo asali daga harin ba-zata da kungiyar ta kai kan Isra’ila.

Kungiyar Hamas a ranar 7 ga watan Oktoba ta kashe kimanin mutum 1,300 galibi farar hula. Maharan sun kuma yi garkuwa da mutum 250 a Gaza.

Afirka ta Kudu wadda ke goyon bayan Falasdinawa ta nemi kotun ta dauki wasu matakai tara ciki har da dakatar da ayyukan soji da Isra’ila take a Gaza. Sai dai ba a tsammanin yanke hukunci a kan wannan na dogon lokaci, watakila shekaru.

Isra’ila ta fusata da zarge-zargen kisan kiyashi inda ta zargi Afirka ta Kudu da sauya gaskiya. Ta ce tana da ikon kare kanta kuma tana kai hare-hare ne kan mayakan Hamas ba wai farar hula Falasdinawa ba.

Ta bukaci alkalai ta yi watsi da bukatar Afirka ta Kudu inda ta ce zarge-zargen ba su da tushe bare makama.

Dole ne alkalai 17 da za su saurari karar su amsa tambayoyi biyu:

  • Na farko, ko Afirka ta Kudu tana da hurumin da zai nuna cewa za a iya hukunta Isra’ila karkashin yarjejeniyar hana kisan kiyashi ta 1948. Yarjejeniyar da Isra’ila da Afirka ta Kudu suka sa wa hannu.
  • Na biyu, ko akwai hadarin illata Falasdinawa a Gaza idan sojojin Isra’ila suka ci gaba da kai hari.

opra news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp