Kotun Ƙoli ta ayyana umarnin gwamnati da shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya bayar na bai wa kotuna da majalisun jiha ‘yancin cin gashin kansu a matsayin wadda ta saɓa wa kundin tsarin mulki.
Buhari ya saka wa dokar mai laƙabin Executive Order 10 hannu ranar 22 ga watan Mayun 2020 da zimmar bai wa ɓangaren shari’a na jihohi 36 da kuma majalisun dokoki ‘yancin cin gashin kansu ba tare da sa hannun gwamnatin jiha ba.
Hakan na nufin babban akanta na ƙasa zai iya tura wa kotunan da majalisun kasonsu na kuɗi kai-tsaye daga asusun gwamnatin tarayya. A cewar BBC.
Sai dai shida cikin bakwai na alƙalan kotun sun amince cewa shugaban ƙasar ya wuce ƙarfin ikonsa da kundin tsarin mulkin ya ba shi wajen bayar da umarnin, saboda haka suka ce ta saɓa wa doka.
A wata shari’ar ta daban a yau Juma’a, kotun mafi girma a ƙasar ta kori ƙarar da gwamnoni suka shigar da gwamnatin tarayya suna neman ta biya su naira biliyan 66 da suka kashe wajen tafiyar da kotunan da kuma manyan ayyuka.