Wata kotun majistare da ke zamanta a jihar Kogi, a ranar Alhamis, ta kori wasu masu fafutukar kare hakkin bil’adama biyu, wadanda jihar ke tuhumar su da laifin lika allunan ‘Buhari must Go’ a watan Afrilun 2021.
Alkalin kotun Mai shari’a Tanko Muhammed, ya yi watsi da karar Amini Udoka da Emmanuel Larry mai lamba: CMCL/123m/2021 bayan an dage sauraron karar.
Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba Edeh, ya ce, an kama mutanen biyu ne a ranar 5 ga Afrilu, 2021, bisa zarginsu da gudanar da yakin neman zaben shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a Lokoja, babban birnin jihar.
Rahotanni sun ce wasu ’yan daba sun yi musu bulala kuma sun shafe kwanaki 78 a tsare kafin a bayar da belinsu.