Kotu a Kenya ta fara zaman sauraron karar zaben shugaban kasa da ke kalubalantar sakamakon zaben 9 ga watan Agusta.
Lauyoyin da ke wakiltar daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasar, Raila Odinga na gabatar da kararsu na neman soke nasarar da William Ruto ya samu a matsayin zabbabben shugaban kasar.
Lauyoyin Mista Ruto da kuma wadanda ke wakiltar hukumar zaben za su bayyana a gaban kwamitin alkalai bakwai .
A halin yanzu, ana bincike da sake kirga kuri’u a rumfunan zabe 15 da aka kalubalanci sahihancinsu a kotu.
Al’ummar Kenya na bibiyar sauraron karar da ake watsa wa a gidajen talabijin din kasar.
Ana sa ran yanke hukunci a ranar 5 ga watan Satumba.


