fidelitybank

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Date:

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano, ƙarƙashin jagorancin mai shari’a Malam Sani Tanimu Sani Hausawa, ta bayar da umarnin a kamo Dagacin garin Tamburawa, dake ƙaramar hukumar Dawakin Kudu, Alhaji Auwal Umar Dantube, bisa kin bayyana a gaban kotu.

An gurfanar da Dagacin tare da wani yaron sa, Sulaiman Dogo Matage, bayan iyalan marigayi Alhaji Mammada Tamburawa sun shigar da ƙorafi akan su a ofishin ‘yan sanda na Zone One, inda suka zarge su da bata suna, cin dukiya ba bisa ka’ida ba da kuma tayar da hankalin jama’a.

Sai dai da sanyin safiyar ranar zaman shari’ar, lauyan da ke kare Dagacin, Barrister Tijjani Kabir Dukawa, ya kai shi kotu kafin ‘yan sanda su kamo shi. Bayan karanta masa tuhumar da ake yi masa, ya musanta laifin, inda lauyansa ya roƙi a bayar da shi a beli.

Mai shari’a ya amince da bayar da belin bisa sharuddan ya kawo mutane biyu masu tsaya masa, wanda zasu kasance ɗaya daga cikin iyalansa ko matarsa, ɗaya kuma daga mai unguwa ko wani dagaci a ƙarƙashin Hakimin Dawakin Kudu. Haka kuma dole ne wanda zai tsaya masa ya gabatar da takardar ɗaukar aiki daga gwamnati, da katin shaida na aiki.

Kotun ta bada umarnin a tsare shi har sai an cika waɗannan sharudda, sannan ta dage cigaban shari’ar zuwa ranar 28/08/2025 domin masu ƙara su gabatar da shaidu.

Bayan zaman kotun, ƙoƙarin jin ta bakin lauyan Dagacin ya ci tura. Sai dai ɗaya daga cikin marayun da suka shigar da ƙara ya shaida cewa suna roƙon kotu ta karɓo musu hakkinsu da suka ce dagacin ya cinye, domin a cewarsa Dagacin bai da wani ikon da zai tauye musu hakkinsu.

naija news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

An Kama wakilin jam’iyya da Naira miliyan 25.9 na Siyan Kuri’a

Jami’an tsaro sun kama wani da ake zargin wakilin...

Farashin kayan abinci na rugu-rugu a Najeriya – NBS

Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta ce hauhawar farashin...

Kotun Kano ta ce a kamo mata Dagacin Tamburawa

Kotun Shari’ar Musulunci da ke shelkwatar Hisbah a Kano,...

Kotu ta ƙwace motocin gwamnatin Zamfara guda 40 daga hannun Matawalle

Kotun Daukaka Kara da ke a Sokoto ta tabbatar...

A na cigaba da gudanar da zaben cike gurbi harda Kano

Kano na ɗaya daga cikin jhihohin da ake kaɗa...

Mutane 12 sun mutu a wani hatsari a Kano – FRSC

Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) reshen Kano, ta...

Masarutar Rano ta haramta aurar da Yaran da ba su kammala karatun Firamare ba

Masarautar Rano a Kano ta haramta cire yarinya daga...

Matatar Dangote za ta fara jigilar mai kyauta ga gidajen mai

Matatar man Dangote za ta fara jigilar mai kyauta...

An sassata rikicin da aka shafe shekaru 30 kan Masallacin Sharada da Islamiyya

Tsohon dan takarar gwamnan Kano, Malam Sha’aban Ibrahim Sharada,...

Duk da kalubalen ‘yan siyasa a Kano mun shirya a zaben cike gurbi – INEC

Kwamishinan hukumar zaɓe mai zaman kanta (INEC) reshen jihar...

Barau ya jagorancin gangamin zaben cike gurbi a Kano

Barau ya samu rakiyar Karamin Ministan Gidaje da Raya...

Gwamnatin Kano ta kara fadada shirin matasa 

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano ya sake,...
X whatsapp