Wata babar kotu da ke Kano ta sake aike wa da Mubarak Bala gidan yari, saboda rashin gabatar wa kotu kwararan hujojin da za su gamsar da ita cewar ba shi da lafiya.
An kama shugaban kungiyar wanda ba su yarda da addini ba ta Najeriya Mubarak Bala, a ranar 28 ga watan 2020 a gidansa da ke jihar Kaduna, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu a Kano, bisa zargin aikata sabo ta hanyar wallafa wasu kalamai a shafinsa na Facebook.
Ya musanta zargin yin batanci ga addini da ake masa.
Ana sa ran ci gaba da shari’ar zuwa ranar Talata