An tuhumi mai shafin sada zumunta na Telegram, Pavel Durov, a Faransa a wani ɓangare na bincikensa kan aikata manyan laifuka.
An bayar da belin hamshakin attajirin ɗan asalin ƙasar Rasha kan Dala miliyan biyar da rabi, tare da hana shi barin Faransa.
Mista Durov na fuskantar tuhume-tuhume da dama da suka haɗa da gazawa wajen daƙile ayyukan ƴan ta’adda da abubuwan da ba su dace ba a dandalin musamman yaɗa hotunan cin zarafin yara.
Wakiliyar BBC ta ce kusan mutum biliyan ɗaya ne ke amfani da dandalinsa na Telegram.
An dai tsare Mista Durov ne tsawon kwana huɗu, inda tuni lauyansa ya yi watsi da zarge-zargen da ake masa, inda ya ce dandalin na Telegram ya kiyaye dokoki da sharuɗɗan amfani da intanet na Turai