Wata kotu a birnin New York ta yanke hukuncin cewa tsohon shugaban kasar Donald Trump ya zuzuta bayanan da ya bayar kan dukiyarsa.
Alkalin Arthur Engoron ya ce Mista Trump ya yi karin gishiri da kambama arzikinsa, inda ya rika kiran kansa a matsayin hamshaƙin biloniya domin samu rance mai sauki da kuma inshora.
A don haka alkalin ya soke lasisin kasuwancisa a birnin na New York.
Sai dai Trump fitar da wata sanarwa inda ya yi Allah-wadai da hukuncin alkalin, da ya kira mara kan gado.
An daɗe ana tuhumar Mista Trump a kan harkokin kasuwancinsa, da na iyalansa