Jihar Maine ta zama jiha ta biyu a Amurka da ta hana Donald Trump tsayawa takara a zaɓen fidda gwani na jam’iyyar Republican domin neman kujerar shugaban ƙasa.
Babbar jami’ar zaɓen Jihar ta ce an dakatar da tsohon shugaban ƙasar ne a ƙarƙashin wata ƙa’idar tsarin mulki da ta haramta wa masu tayar da ƙayar baya rike muƙami, saboda abubuwan da ya gudanar gabannin tarzomar da aka yi a majalisar dokokin Amurka a shekarar 2021.
Kwamitin yaƙin neman zaɓen Trump ya kira matakin a matsayin cin zarafi ga dimokraɗiyyar Amurka tare da cewa za a shigar da ƙara cikin gaggawa.
A makon da ya gabata aka dakatar da Mista Trump shiga zaɓen fidda gwanin jam’iyyar a jihar Colorado saboda irin dalilan da Jihar Maine ta bayyana.


