Babbar kotun tarayya ta kori dan majalisa mai wakiltar mazabar Mubi ta kudu a majalisar dokokin jihar Adamawa, Honarabul Musa Umar Bororo.
Babbar kotun tarayya ta biyu da ta zauna a Yola ranar Litinin, ta umurci dan majalisar da ya bar kujerarsa ba tare da bata lokaci ba saboda ficewa daga jam’iyyar da ya lashe zaben majalisar.
A watan Afrilun bara ne dai Bororo ya fice daga jam’iyyar adawa ta APC a jihar ya koma jam’iyyar PDP mai mulki.
Babbar kotun da ke karkashin mai shari’a Saleh Kogo, ta yanke hukuncin cewa Bororo wanda ya shiga majalisar ne a karkashin jam’iyyar APC, bai kamata ya koma PDP ya ci gaba da zama a kan mukaminsa ba.
Sai dai mai shari’a Kogo, ya yi watsi da karar da aka shigar a gaban mamba mai wakiltar Mubi ta Arewa, Hon Shuaibu Dan Musa da mamba mai wakiltar Fufure/Gurin, Hon Shuaibu Babas wanda shima ya sauya sheka daga APC zuwa PDP a lokuta daban-daban.
Ya ce jam’iyyar APC ta kasa tabbatar da shari’ar da ta ke a kan mutanen biyu.
A watan Oktoban shekarar da ta gabata ne dai shugabannin jam’iyyar APC na jihar suka maka ‘yan majalisar uku a gaban kuliya saboda sun fice daga jam’iyyar PDP, inda suka bukaci kotun da ta ba da umarnin cewa majalisar ta zama doka ta bayyana kujerunsu.