Kotun ɗaukaka ƙara da ke Abuja, ta tabbatar da nasarar zaɓen gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi.
Alkalan kotun guda uku, dukkansu sun amince tare da tabbatar da cewa Bala Mohammed ne ya samu nasara a zaɓen ranar 18 ga watan Maris.
A karar da jam’iyyar APC ta shigar, ta roki a soke zaɓen saboda ba a cike fom da takardun da aka yi amfani da su a zaɓen yadda ya kamata ba.
Kotun ta yanke hukuncin cewa wanda ya shigar da kara ya kasa tabbatar da wannan zargi, da mazaɓun da abin ya faru, da kuma rashin gamsassun hujjoji