Kotun Ƙolin Brazil ta bayar da umarnin toshe dandalin sada zumunta na Telegram a faɗin ƙasar.
Alƙali Alexandre de Morais ya ce kamfanin Telegram ya nuna raini ƙarara ga tsarin shari’ar Brazil.
Wakilin BBC ya ce a taƙaice alƙalin ya yanke hukunci kan cewa kamfanin ya ƙi rufe wasu shafuka da ke yaɗa labaran ƙarya duk da an ba shi umarnin rufe su a baya.
Shugaban Brazil Jair Bolsonaro magoya bayansa na amfani da dandalin kuma ana zargin manhajar ta bayar da dama ga masu safarar ƙwayoyi da masu laifi su aikata laifuka.
Sai dai Mista Bolsonaro ya yi kakkausar suka ga alƙalin da ya yanke hukuncin.