Kotun Ƙoli ta tabbatar da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara, da ya tabbatar da zaɓen Sanata Ademola Adeleke a matsayin gwamnan jihar Osun.
Mai shari’a Emmanuel Akomaye Anyim ne ya karanto hukuncin da rukunin alƙalan kotun biyar suka saurara a ƙarar da tsohon gwamnan jihar, Gboyega Oyetola ya ɗaukaka.
Tun a baya ne dai Sanata Ademola Adeleke ya samu nasarar lashe zaɓen gwamnan jihar Osun a jam’iyar PDP, bayan ya doke tsohon gwamnan jihar, Gboyega Oyetola.