fidelitybank

Kano: Kotu za ta yanke hukuncin shugabancin jam’iyar APC

Date:

A yau Talata ne ake sa ran Kotun Ɗaukaka Ƙara dake birnin tarayya, za ta yi zaman sauraron ƙarar rikicin shugabanci a jam’iyyar APC mai mulkin Jihar Kano, tsakanin Gwamna Abdullahi Ganduje da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau.

Ɓangaren Gwamna Ganduje ne ya ɗaukaka ƙarar bayan bayyana tsagin Shekarau a shari’o’i biyu da suka gabata, inda yake neman a soke shugabancin Ahmadu Haruna Zago, wanda ke samun goyon bayan tsohon Gwamna Shekaru, sannan a bayyana Abdullahi Abbas a matsayin halastaccen shugaba.

A wata shari’ar ta kotun tarayya na baya, kotun ta bayyana cewa, ɓangaren Ganduje ba shi da hurumin neman a kori ƙarar, saboda ya riga ya ɗaukaka ƙara, saboda haka ne kuma ta yi watsi da buƙatarsu.

Rikicin APC a Kano ya samo asali ne tun bayan gudanar da tarukan jam’iyyar a matakin mazaɓu da jiha, abin da ya haddasa aiwatar da taruka biyu ƙarƙashin Sanata Ibrahim Shekarau da kuma ɓangaren gwamnatin Kano.

nnn-news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...

A sake sabon tsarin shugabancin INEC a Najeriya – Goodluck

Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan, ya yi kira da...

Magoya bayan West Ham ku hada kai da Bowen – Potter

Mai horas da West Ham, Graham Potter ya bukaci...

Alhaki na ne kifewar jirgin kasa – Shugaban Hukumar

Shugaban hukumar jiragen ƙasa ta Najeriya (NRC), Kayode Opeifa,...

Tinubu ya haramta fitar da ɗanyen man kaɗanya

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin dakatar...

Hisba ta karɓi ƙorafe-ƙorafe 83,776 a Kano

Rundunar Hisbah ta jihar Kano ta bayyana cewa, a...

Ganduje ba dan cin hanci ba ne – Martanin Garba Ga Gwamnatin Kano

Tsohon kwamishinan yaɗa labarai na Jihar Kano, Muhammad Garba,...

Kungiyar Malaman Jami’o’i bangaren BUK sun yi zanga-zangar Lumana

Kungiyar Malaman Jami’o’i (ASUU), reshen Jami’ar Bayero Kano (BUK),...
X whatsapp