fidelitybank

Kotu za ta yanke hukuncin karshe tsakanin Fubara da APC

Date:

A yau Laraba ne kotun koli za ta yanke hukunci kan takaddamar da ake yi game da zaben gwamnan jihar Ribas.

Lamarin dai na tsakanin Gwamna Siminalayi Fubara na jam’iyyar PDP da Tonye Cole na jam’iyyar APC.

A makon da ya gabata ne alƙalai biyar na Kotun Koli karkashin jagorancin Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun suka saurari lauyoyin bangarorin biyu.

Bangarorin sun samu sanarwa daga babbar kotun cewa za a yanke hukuncin a ranar Laraba.

Cole yana kalubalantar nasarar Gwamna Fubara a zaɓen gwamna da aka yi a ranar 18 ga watan Maris na 2023 da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar a jihar.

A sakamakon zaɓen, Fubara ya samu kuri’u 302,614 inda ya doke abokin hamayyarsa, Tonye Cole wanda ya samu kuri’u 95,274.

Ganin haka ne ɗan takarar jam’iyyar APC ɗin ya ce an tafka maguɗi a zaɓen inda ya kuma ce Fubara bai cancanci tsayawa takarar ba saboda a lokacin yana kan muƙamin Akanta-Janar na jihar Ribas,kuma hakan ya saɓa wa kundin tsarin mulkin ƙasar domin ya kamata ya fara yin murabus kafin tsayawa takara.

Bayan haka ne Cole ya kai maganar gaban kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamna inda ya nemi a tsige Fubara, amma aka yi watsi da ƙarar wanda hakan ya sa ya sake kai karar zuwa kotun ɗaukaka ƙara inda ita ma ta yi watsi da ƙarar tasa.

Ana sa ran kawo karshen takaddamar a hukuncin da kotun kolin za ta yanke a yau.

legit.ng.news.

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp