fidelitybank

Kotu za ta yanke hukunci a kan wanda ya kashe dalibar makaranta a Kano

Date:

A ranar Alhamis ne ake sa ran wata babbar kotun jihar Kano, za ta yanke hukunci bisa kisan da aka yi wa wata karamar yarinya Hanifa Abubakar.

Ana zargin malaminta Abdulmalik Tanko  ne ya sace ta a watan Dasambar 2021 tare da kashe yarinyar mai shekara biyar, kana ya binne gawarta a gidansa.

Kisan nata ya ja hankalin duniya inda dubban mutane, ciki har da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, suka yi tur da shi.

Bayanai sun tabbatar da cewa wasu mutane ne suka ɗauke ta a babur mai kafa uku da ake kira A-Daidaita-Sahu bayan ta dawo daga makaranta a kan hanyarta ta zuwa gida inda suka tafi da ita.

An yi ta nema da cigiya amma sai bayan kwana 46 aka ji ɗuriyarta.

A watan Janairu ne aka gano gawar yarinyar da aka sace a ranar 4 ga watan Disambar 2021.

‘Yanda sanda sun tono gawarta tata wadda ake zargi Abdulmalik Tanko, mai makarantar  Noble Kids Academy, ya binne a wani rami.

An zarge shi da hada baki da Isyaku Hashim da matarsa Fatima Jibril da laifukan da suka hada da hada baki wajen aikata laifi, da satar mutum da kuma tsare yarinyar da suka sace ba tare da amincewarta ba da kuma kisan kai.

Sai dai kotu ta bayar da umarnin sakin Fatima Jibril bayan ta yi nasarar wanke kanta daga zarge-zargen a gaban kotu.

An kwashe kimanin watanni shida ana shari’ar wadda Mai Shari’a Sulaiman Na’abba yake jagoranta. In ji BBC.

news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp