Wata kotu a Amurka ta ce, za ta sake nazarin zargin cin zarafin lalata da ƙananan yara da wasu mutum biyu ke yi wa shahararren mawaƙin nan ɗan ƙasar Amurka – da ya rasu – Michael Jackson.
Mutanen biyu – waɗanda a yanzu shekarunsu 40 – sun shigar da ƙarar kamfanin mawaƙin, inda suke zargin Michael Jackson da cin zarafinsu ta hanyar lalata a lokacin da suke ƙananan yara.
Wade Robson da James Safechuck, a yanzu kotu za ta saurari ƙarar da a baya wata kotu ta yi watsi da ita.
Mutanen biyu sun ce haƙƙin kamfanonin mawaƙin ne su kare su a lokacin da abin ya faru.
Lauyoyin Michael – wanda ya rasu a shekarar 2009 – sun ce bai aikata laifin ba.
Rabson da Safechuck sun zargi Michael Jackson da cin zarafinsu a shekarun 1980 da 1990 a lokacin da suke zaune a gidan gonarsa da ke Neverland.
An bayyana zargin a cikin wani film da aka yi kan rayuwarsa a 20019 mai suna ‘Leaving Neverland’, fim ɗin da iyalan Micheal suka bayyana da ɓata-sunan marigayin
A 2012 kuma alƙalin ya zartar da irin wannan hukunci kan Mista Robson saboda irin waɗannan hujojoji.
To sai dai a ranar Juma’a wata kotun ɗaukaka ƙara a California ta warware hukuncin na baya, tana mai cewa dole ne kamfanin na sauke nauyin da ke kansa na kare haƙƙin ƙananan yara.
“Ba zai yiwu a ƙyale kamfani ya riƙa dillancin lalata ƙananan yara ba, don kawai mamallakin kamfanin ake zargi da aikata laifin”, in ji kotun.
Ta ƙara da cewa ”sakaci ne kamfanin ya ɗauka ba shi da haƙƙin kare ƙananan yara, don haka wannan kotu za ta sake nazarin wannan sharia’a domin yiyuwar tuhumar kamfanonin”.
Lauyan mutanen biyu, Vince Finaldi, ya ce kotu ta yi watsi da hukuncin farko wanda ya saɓa wa dokokin Carlifornia.
A nasa ɓangare, lauyan Micheal Jackson, Jonathan Steinsapir, ya ce yana da yaƙinin cewa wanda yake karewa bai aikata laifin ba.
Ya ci gaba da cewa duka zarge-zargen sun saɓa wa ƙwararan hujjojin da suke da su. In ji BBC.