fidelitybank

Kotu za ta duba yuwar bayar da belin Yahaya Bello

Date:

Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello tare da wasu mutane biyu da Hukumar EFCC ta gurfanar a gaban kotu a yau Laraba sun musanta zarge-zargen rashawa na Naira biliyan 80 da ake yi musu.

Yahaya Bello, wanda shi ne na farko a cikin mutanen da ake tuhuma tare da sauran mutanen biyu Shuaibu Oricha da Abdulsalami Hudu, sun musanta duka tuhuma 16 da aka fara karanto musu a gaban mai shari’a Maryanne Anenih ta babbar kotun ta Abuja.

Joseph Daudu, (SAN – babban lauya) shi ne jagoran lauyoyin da ke kare toshon gwamnan da sauran waÉ—anda ake tuhuma, yayin da Kemi Pinhero (shi ma babban lauya – SAN), ke jagorantar masu gabatar da Æ™ara.

Bayan musanta aikata laifukan, lauyan waÉ—anda ake tuhumar ya nemi a bayar da belin Bello amma lauyan EFCC ya nemi kada a bayar da cewa wa’adi ya wuce tun watan Oktoba.

To amma bayan sauraron ɓangarorin biyu kotun ta tsayar da ranar 10 ga watan Disamba mai kamawa domin duba buƙatar belin.

EFCC ta yi nasarar gurfanar da tsohon gwamnan na jihar ta Kogi a gaban kotun ta tarayya da ke Abuja a yau Laraba bayan wata da watanni na gaza hakan, kasancewar ya ƙi amsa gayyatar hukumar kuma duk yunƙurinta na kama shi ya ci tura.

A jiya Talata ne aka ce tsohon gwamnan ya kai kanshi hukumar ta EFCC da rakiyar lauyoyinsa – amma daga baya hukumar ta ce tana tsare da shi.

vgn news 2022

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp