Kotun daukaka kara da ke zamanta a Yola a ranar Alhamis, ta yi watsi da hukuncin da babbar kotun kasar ta yanke wanda tun farko ta soke zaben fidda gwanin da ya kai Emmanuel Bwacha da Aishatu Binani a matsayin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na jihohin Taraba da Adamawa.
A ranar Alhamis ne kotun ta bayar da umarnin a mika sunayensu ga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) a matsayin ‘yan takarar gwamna na jam’iyyar APC na jihohin biyu.
DAILY POST ta tuna cewa a watan Satumba mai shari’a Simon Amobeda na wata babbar kotun tarayya da ke Jalingo, babban birnin jihar Taraba, ya kori Bwacha bayan wani dan takara David Kente ya shigar da kara.