Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta shaida wa kotun sauraron kararrakin zaben shugaban kasa da ta yi watsi da bukatar da jamâiyyar Labour Party, LP, da dan takararta na shugaban kasa, Peter Obi, suka shigar, na neman a nuna yadda abin ke gudana a talabijin.
Lauyan Obi da LP Levy Ozoukwu, ya shaida wa manema labarai bayan zaman da aka yi a ranar Larabar da ta gabata cewa INEC ta ki amincewa da bukatar su na watsa shirye-shirye kai tsaye.
Ozoukwu ya ce: âAbin mamaki, INEC na adawa.
âCibiyar gwamnati da gwamnati ke ba da tallafi kuma tana wakiltar jama’a tana cewa ba sa son jama’a su ji daÉin watsa shirye-shiryen kai tsaye. Me suke boyewa?â
Obi da LP sun shigar da karar suna kalubalantar nasarar dan takarar jamâiyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu a zaben 2023.
Masu shigar da kara na neman kotun da ta bayyana Obi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa ko kuma a madadin INEC ta sake gudanar da sabon zabe.