Kotun daukaka kara ta yi watsi da bukatar biyan Sunday Igboho naira biliyan 20 saboda asarar da ya yi a gidansa.
Da yake yanke hukunci a karar da babban attoni janar na kasa da hukumar kula da tsaron farin kaya da daraktan hukumar a jihar Oyo suka shigar a kan hukuncin mai shari’a Muslim Hassan na babbar Kotun Jihar Oyo ya yanke na cewa hukuncin da mai shari’a Ladiran Akintola, ya yanke na cewa a biya Igboho kudin ya sabawa ka’ida.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa a ran 17 ga watan Satumban 2021, mai shari’a Akintola ya bukaci a biya Igboho naira biliyan 20 a matsayin kudin asarar kayaki da ya yi a gidansa bayan hari da ya yi zargi ‘yan bindiga suka kai masa ranar 1 ga watan Yuli wadda kuma ya sabawa umurnin babban attoni janar na kasa, Abubakar Malami da kuma hukumar tsaron farin kaya da suka kalubalanci hukuncin.
Mai shari’a Hassan ya ce babu wasu hujjoji da suka marawa hukuncin babbar kotun jihar ta Oyo.
Ya ce mai shari’a Akintola bai gano asarar da Igbohon ya ce ya yi ba a tsawon bincikensa, inda ya kara da cewa babu kwararan hujjoji da suka nuna yawan asarar da Igbohon ya yi a gidansa.
Mai shari’a Hassan ya kuma kara da cewa ba wata hujja ko bincike da ta nuna mutum biyu sun mutu yayin hari a gidan dan gwagwarmayar kamar yadda ya yi ikirari.