Wata kotu a kasar Norway ta yi watsi da bukatar neman belin mai kisan gillar nan Anders Behring Breivik, a wani hukunci da ta yanke ranar Talata, inda ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan yari.
Breivik, mai kyamar musulmi neo-Nazi, ya kashe mutane 77 a wani mummunan kisan gilla da aka yi a kasar Norway a watan Yulin 2011. Ya kashe takwas da bam a cikin mota a Oslo, sannan ya bindige 69, yawancinsu matasa, a sansanin matasa na jam’iyyar Labour.
A ranar farko ta zaman kotun a watan da ya gabata, Breivik ya yi wata alama ta farar kishin kasa da yatsunsa kafin ya daga hannunsa na dama cikin gaisuwar ‘yan Nazi, domin nuna akidarsa ta dama a lokacin da ya shiga kotun.
Breivik, mai shekaru 42, ya na zaman hukuncin daurin shekaru 21 a Norway, wanda za a iya tsawaita shi har abada, idan har aka dauke shi a matsayin ci gaba da barazana ga al’umma.