Wata kotun soja a Burkina Faso ta yanke wa tsohon Shugaban Ƙasa Blaise Compaore hukuncin ɗaurin rai-da-rai sakamakon kama shi da hannu a kisan wanda ya gada Thomas Sankara.
An yi wa Compaore shari’a a bayan idonsa yayin da yake gudun hijira yanzu haka.
An yanke wa tsohon shugaban sashen tsaro na gwamnatinsa, Hyacinthe Kafando, hukuncin ɗaurin rai-da-rai shi ma.
Sankara wanda ɗan neman sauyi ne mai aƙidar Markisanci, wasu ‘yan bindiga ne suka harbe shi a babban birnin ƙasar Ouagadougou a 1987.