Wata babbar kotu da ke Yola a jihar Adamawa, ta kori Elisha Abbo a matsayin dan takarar Sanatan Adamawa ta Arewa a zabe mai zuwa.
Kotun ta kuma hana jam’iyyar All Progressives Congress (APC) amincewa da shi a haka.
Mai shari’a Danladi Mohammed ne ya yanke hukuncin a ranar Litinin. Mai shari’a Danladi ya yanke hukuncin cewa Sanata Abbo bai cancanci sake tsayawa takara ba tunda jam’iyyar ta kore shi.
Alkalin ya kuma bayyana cewa Sanatan da jam’iyyar APC na da nasaba da kudurin shugabannin kananan hukumomin Mubi ta Arewa na jam’iyyar mai kwanan wata 7 ga watan Oktoba 2022, wanda ya kori dan majalisar; don haka bai cancanci ya ci wani hakki ko wata gata da aka ba ‘yan APC ba.
Sannan ya bukaci Sanata Abbo da ya daina bayyana kansa a matsayin dan takarar jam’iyyar na shiyyar.
A halin da ake ciki, Sanatan da ke cikin rudani ya caccaki hukuncin, inda ya bayyana shi a matsayin hukuncin daurin talala.