fidelitybank

Kotu ta yankewa makiyayi hukuncin daurin shekaru 7 tare da zabin tara

Date:

Wata kotun Majistare da ke Abeokuta a jihar Ogun a ranar Alhamis ta yanke wa wani makiyayi mai suna Abdulahi Adamu mai shekaru 38 hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari, bisa samunsa da laifin zamba da satar shanun da suka kai sama da Naira miliyan 43.

Adamu an yanke masa hukunci ne bisa wasu tuhume-tuhume guda uku da suka hada da hada baki, zamba da kuma sata.

Da take yanke hukuncin, mai shari’a Olajumoke Somefun, ta ce, dukkan shaidun da masu gabatar da kara suka gabatar sun tabbatar da babu shakka cewa, wanda ake tuhuma yana da laifi kamar yadda ake tuhumarsa.

Somefun ta bayyana cewa bayan gano wanda ake tuhumar yana da laifi kamar yadda ake tuhumarsa, amma ta yanke masa hukuncin daurin shekaru bakwai a gidan yari tare da zabin tarar Naira dubu 250,000.

Ta kara da cewa za a fara amfani da zabin tarar ne idan aka dawo da duk wasu shanu 259 da wanda aka yankewa laifin ya sace.

Tun da farko, mai gabatar da kara, ASP Olakunle Shonibare, ya shaida wa kotun cewa, wanda ake tuhuma ya aikata laifin ne a ranar 12 ga watan Satumba a kauyen Alamutu ta hanyar shataleyalen, a Abeokuta.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp