Wata kotu a birnin Legas ta yanke wa dan sandan da ya kashe matashin nan Kolade Johnson daurin rai da rai a gidan yari.
Shekaru uku kenan da dan sanda ya harbe matashin, wanda masoyin kwallon kafa ne, yayin wata hatsaniya a wani gidan kallo ranar 31 ga watan Maris din 2019.
Kisan Kolade Johnson ya haddasa zanga-zanga a Legas, wadda ta ja hankalin Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin.
Kazalika kisan na daga cikin abubuwan da suka haddasa kazamar zanga-zangar kyamar cin zarafin da ‘yan sanda suke yi wa jama’a ta EndSars.
A wani bangaren, wata kotun a birnin Port Harcourt ta yanke hukuncin kisa kan wani dan sanda ta hanyar rataya, bayan ta kama shi da laifin kisan wani direba a kan naira 100 a 2015.
Mai shari’a Elsie Thompson ta ce da gangan James Imhalu ya harbi David Legbara kuma ya kashe shi, kamar yadda shaidu suka tabbatar.