Wata kotu a Pakistan ta soke hukuncin da aka yankewa tsohon Firaiministan ƙasar, Imran Khan da matarsa a bisa aure ba kan ƙa’ida ba.
A watan Fabrairu aka yankewa Mr Khan da matarsa Bushra Bibi hukuncin shekara bakwai a gidan yari bayan an samu matar da laifin kasa jira ta yi idan kafin auren su, duk da cewa ta fito ne daga wani gidan aure, lamarin da ya saɓa dokokin addininin musulumci.
Alƙalin kotun ya yanke hukuncin cewa a saki waɗanda ake zargin idan dai babu wata tuhuma ta daban da ake masu.
Amma jam’iyyar PTI ta Imran Khan ta ce ba za a sake shi ba saboda akwai sauran tuhumar da ake masa a kotun sauraron ƙarar ta’addanci.
Mr Khan ya shafe kusan shekara ɗaya yana tsare a gidan yari a kan zarge-zargen da ya ce duk bita da ƙullin siyasa ne kawai.


