Wata kotun yanki da ke zamanta a Bukuru, karamar hukumar Jos ta Kudu a jihar Filato, ta umurci ‘yan sanda da su kwace dukkanin sakatarorin kananan hukumomi 17 da ke jihar.
Tun a watan Yuni ne kwamishinan ‘yan sandan jihar Bartholomew Onyeka ya rufe dukkan sakatarorin, bayan dakatar da zababbun shugabanni da kansiloli da Gwamna Caleb Mutfuwang ya yi.
Kwamishinan ya ce an rufe sakatarorin ne domin hana tauye doka da oda daga magoya bayan jam’iyyar.
Sai dai mai shari’a H. H. Dolnaan a hukuncin da ya yanke a ranar Litinin ya bayar da umarnin wucin gadi na tilastawa CP Bartholomew Onyeka.
ya umurci mutanensa da su gaggauta ficewa daga dukkan sakatarorin domin baiwa ma’aikata damar ci gaba da aiki.
Kotun ta sanya ranar 7 ga watan Agusta domin gabatar da karar da kuma sauraron karar.
Umurnin ya biyo bayan takardar da D. P. Dusu ya shigar a cikin kara mai lamba: ACB/CV/106/2023 da babban mai shari’a na jihar Filato ya gabatar a kan CP.