Kotu a New York ta umarci tsohon shugaban Amurka, Donald Trump ya biya diyyar dala miliyan 83 ga wata marubuciyya kan laifin bata mata suna.
An samu Mista Trump da bata sunan Elizabeth Jean Carroll a wani furuci da ya yi lokacin da yake kan mulki a shekara ta 2019.
Ms Carroll ta shaida cewa kalaman Mista Trump sun zubar mata da mutuncinta da kasance babban barazana a gareta, bayan ya shaida cewa ta tafka karya a zargin cin zarafinta ta hanyar lalata shekaru kusan 30 da suka gabata.
Donald Trump ba ya kotun a lokacin yanke wannan hukunci, sai dai tsohon shugaban ya musanta alaka ko sanin Jean Carroll.