Wata babbar kotun tarayya da ke Kubwa a Abuja, a ranar Larabar da ta gabata, ta umarci wani matashi dan shekara 30 da haihuwa wanda yake yi wa kasa hidima mai suna Chibuike Omemgboji, da ya share harabar Cocin Winners Chapel, Jahi, Abuja na tsawon watanni shida.
Omemgboji ya amsa laifin damfarar da Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) ta shigar inda ya roki kotun da ta yi masa sassauci.
Da yake yanke hukuncin, mai shari’a Kezziah Ogbonnaya, ya umarci Omemgboji da ya kai rahoto ga cocin a kullum daga ranar 15 ga watan Yuni, ya shiga da fita bayan ya kammala hidimar.
Sai dai Ogbonnaya ya gargade shi da ya daina aikata laifuka kuma ya kasance da kyawawan halaye.
Lauyan tsaro, Mista Eteh Enobong, ya shaida wa kotun cewa Omemgboji, wanda ba a taba yanke masa hukunci a baya ba a Najeriya ko kuma a kasashen waje ya yi nadama kuma ya tuba.