Kotu ta ayyana Alhaji Muhammad Sani Abacha, a matsayin dan takarar jam’iyyar PDP a Kano.
Kotun ta danganta cewa zaben na su shi ne kadai wanda hukumar zabe ta kasa INEC ta halarta.
Alkalin kotun mai shari’a, A.M Liman, a wani hukunci da ya yanke a yammacin ranar Alhamis din nan, ya soke zaben fidda gwanin da ya samar da Sadik Amunu Wali a matsayin dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP tare da umurtar INEC da ta cire sunan Sadiq Wali ta sa na Muhammad Sani Abacha.
An yanke hukuncin ne da misalin karfe 12:00 na rana a yau amma daga baya aka canza lokacin zuwa karfe 4:00 na yamma.
Kotun ta amince da dukkan addu’o’in wanda ya shigar da kara a cikin karar.