Wata babbar kotun tarayya da ke Osogbo ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Osun da ta dakatar da shirye-shiryenta, ta na gudanar da zaben kananan hukumomi.
OSIEC a ranar 15 ga Agusta, 2022, ta bayyana shirin gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar a ranar 15 ga Oktoba, 2022.
Ya ci gaba da cewa zaben ya yi daidai da sabuwar dokar OSIEC da aka sanya wa hannu.
Sai dai jam’iyyar PDP a jihar ta maka hukumar gaban kotu tare da bayyana shirin kauracewa zaben kansiloli idan OSIEC ta gudanar da zaben.
Jam’iyyar PDP ta Osun ta kuma yi zargin cewa ba lallai ba ne gwamnatin Gwamna Gboyega Oyetola ta gudanar da zaben a yanzu.
Wannan umarnin kotu na zuwa ne bayan hukumar ta fara horas da ma’aikatanta na wucin gadi a zaben kananan hukumomin da za a yi a ranar 15 ga watan Oktoba.