Wata Kotu ta umarci hukumar yaƙi da rashawa ta EFCC ta ƙwace jami’ar Nok mai zaman kanta mallakin wani tsohon babban jami’in gwamnati da ke fuskantar tuhuma kan Rashawa.
EFCC ta ce, Anthony Hassan, wanda tsohon darakta ne na harkokin kuɗaɗe a ma’aikatar lafiya, ya gina jami’ar ne da kuɗin Rashawa.
Sai dai wani abu da ba a fayyace ba, shi ne ko matakin zai shafi karatun ɗalibai a makarantar da ke arewacin Kaduna.
Kuma babu wasu karin bayyanai kan ko Mista Hassan zai ɗaukaka ƙara.
Sannan baya ga ƙwace jami’ar, akwai kadarorinsa da otel din alfarma da aka umarci a karɓe su.
A ‘yan kwanakin nan dai EFCC ta buɗe wuta kan binciken Rashawa a faɗin ƙasar.