Babbar kotu da ke zamanta a Umuahia ta bai wa babban lauyan gwamnati kuma antoni janar na kasar umarnin goge sashe na 84(12) na sabuwar dokar zabe da aka sauya.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa, Mai shari’a Evelyn Anyadike ne ta bayyana hakan a ranar Juma’a inda ta ce, wannan sashe baya cikin kundin tsarin mulkin, bai da ce, da kundin tsarin mulkin ba, kuma ya saba wa doka, ba shi kuma da ta siri kan komai, kuma saba doka ta ko wacce fuska.
Sashen ya ce: “babu wani wanda aka nada a ko wanne mataki da zai zabi wakili ko za a zabe shi a wani taro na ko wacce irin jam’iyyar siyasa a da zimmar tsayawa takarar a ko wanne irin zabe,”
Alkaliyar ta yi bayanin cewa kundin tsarin mulkin na 1999, karkashin sahe na 66(1)(f), 107(1)(f), 137(1)(f) da 182(1)(f) ya riga ya yi bayani a fayyace kan cewa duk wanda ke da mukami a gwamnati da ke neman takara sai ya ajiye mukaminsa da kwana 30 kafin ranar zabe, amma ko wacce irin doka ce ta nemi wadannan masu muka mai su ajiye mukamansu ko kuma su bar ofis a kowanne lokaci kafin wannan lokaci to ta sabawa doka.