A karshe dai kotun koli ta sanya ranar Alhamis 26 ga watan Oktoba domin yanke hukunci na karshe a kararraki biyu da suka rage na kalubalantar halascin ko akasin haka na ayyana shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa da ya gabata.
Koke ne da dan takarar shugaban kasa na jamâiyyar PDP, Atiku Abubakar, da takwaransa na jamâiyyar Labour, LP, LP, Peter Gregory Obi suka shigar.
Daraktan yada labarai na kotun koli, Dr Aemeri Festus Akande, ya tabbatar da faruwar lamarin a ranar Laraba.
Ya ce an samar da isassun tsare-tsare na tsaro domin dakile tabarbarewar tsaro a ciki da wajen harabar kotun.
A ranar Litinin din da ta gabata ne wani kwamiti mai mutum 7 na Alkalan Kotun karkashin jagorancin Mai Shariâa John Inyang Okoro ya dauki hujjar karshe daga lauyoyin ga wadanda suka shigar da kara.


