fidelitybank

Kotu ta tsare Murja ‘yar TikTok a gidan gyaran halin Kano

Date:

Wata kotun shari’a da ke zamanta a unguwar Hausawa Filin Hockey a cikin birnin Kano, ta bayar da umarnin tsare wata shahararriyar mai magana a shafin sada zumunta TikTok, Murja Ibrahim Kunya, a gidan gyaran hali.

A ranar Alhamis din nan ne aka gurfanar da ita a gaban kuliya bisa tuhumar da ake mata na bata suna, rashin mutunci, dagula al’umma da kuma tauye zaman lafiyar jama’a.

An kara zargin bata suna ne a kan karar da wasu Tik Tokers biyu: Aisha Najamu da Idris Maiwushirya suka shigar, inda suka zargi Murja da bata sunan su.

Karanta Wannan: ‘Yan sanda sun cafke Murja ‘yar Tik Tok a Kano

Bayan da lauya mai shigar da kara, Lamido Sorondinki ya karanta wa wadanda ake tuhumar duka tuhume-tuhumen, ta musanta aikata laifin.

Bayan haka, lauyan Murja, Yasir Musa ya gabatar da bukatar neman belin ta, amma lauyan masu gabatar da kara ya ki amincewa da shi.

Alkalin kotun, Abdullahi Halliru, ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wanda ake tuhuma a gidan yari sannan ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 16 ga watan Fabrairu domin yanke hukunci kan neman belin.

Ku tuna cewa a kwanakin baya ‘yan sanda sun kama Murja a Kano bisa umarnin wata kotun Shari’a.

assu update

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp